Yadda Zakiyi Karin Kugu

Kugu a jikin mace abu ne da ya kasance kinada shi ko bakida shi kawai. Saboda yana zuwa ne da halitta ta jiki da yadda yadda jikin yake. 

Duk da haka akwai hanyoyin da ake iya kara musu girma ko su fidda shape.

GA MACEN DAKE BUKATAR KUGU HIPS 

Ki nemi:

  • Ayaba 
  • Abarba 
  • Gwanda 
  • Kankana 
  • Zuma 
  • Madara peak

sai ki hadasu waje daya ki markadasu su zama ruwa sai ki juye wannan madara ki dinga sha bayan sallar asuba.

Ko kuma ki samu dafaffen zogale da alayyahu ki zuba tumatir da albasa suji sosai kiyi kwadonsu ki dinga ci, indai zaki juri yin hakan da sannu zaki ga abin mamaki.

Kisamu dankali na hausa ko na turawa ki dafashi saiki yanyankashi sannan ki dakashi ki zuba acikin nono ko madara peak sannan ki zuba zuma ki gaurayashi sosai kisha zaki iyayinsa sau uku Akowanne sati tabbas wannan hadin har ni ima yana karawa mace.

ko kuma ki samu kankana ki yanyankata da gwanda itama ki fere ta sai kabewa itama ki yankata kokumba (gurji) shima haka da tumatur ki yanyankashi ki wankeshi duk kiyi markadensu waje daya ki tace ruwan kinasha sau biyu a rana Shima wannan yana kara hips sannan yana karawa mace ni ima

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!