AMFANIN LALLEN GARGAJIYA DA YA KAMATA KU SANI MATA

Ga kadan daga cikin anfanin lalle
Ciwon kafa _Yin lalle na rage ciwon kafa. A kwaba lalle da ruwa ya yi kauri, a shafa wa kafar na tsayon lokacin da ake bukata sannan a wanke. Yin haka na rage radadi da zugin da ke damun mutun a kafarsa.
Dattin ciki _ Shan ruwan lalle na wanke dattin dake ciki. Idan aka jiga lalle da ruwa aka tace, sai a sha ruwan daidai gwargwado. Yin hakan na wanke dattin ciki.
GYARAN FATA _ Ana amfani da lalle wajen gyara fatar jiki da kawar da datti da kuma sanya fata haske mai kyau. Domin haka, sai a zuba lalle da ruwa a rika wanka da ruwa lallen akalla so daya a rana.
Fatar fuska _ Lalle na sa fuska ta yi laushi da haske. Bayan an kwaba lallen da kauri a rika goga fuskar ta ita. Bayan minti 20 zuwa 30 sai a wanke fuskar da ruwa. Za a iya yi sau daya zuwa uku a rana.
KURAJEN FUSKA_Ga masu fama da kurajen ‘pimples’ sai su kwaba lalle da ruwan lemon tsami ya yi kauri suka rika shafa kwabin a fuskar. Zuwa wani lokaci pimples din za su bace.
AMOSANIN KAI_Ana a wanke gashin kai da ruwan lalle domin maganin amosarin gashi. Ana yin hakan ne ta hanyar kwaba lalle a ruwa ya yi dan ruwa-ruwa sannan a jika gashin a cikin ruwan. Bayan minti 20 sai a wanke kan. Yawan yin hakan na kashe amosarin kai.
Mungode