ABUBUWAN AMFANI DA SUKA KAMATA KU SANI GAME DA KIRFA KO CINNAMON

CINNAMON

Kirfa na kuma daya daga cikin nau’ukan kayan kamshi da ake amfani da su don kara wa abinci da abin sha kamar su shayi da sauran su karin dandano da kuma kamshi.

Related Articles

Kirfa ko kuma Cinnamon a turance, bawon wata bishiya ne da a kimiyyance ake kira Cinnamomum, kuma da aka fi samu a kasashe kamar su Brazil, Sri Lanka, India, har ma da kasar Masar.

Ana sassako kirfa ne daga bawon cikin wannan bishiya, kamar yadda jaridar kiwon lafiya ta Healthline da ke Birtaniya ta wallafa.

Kirfa na kuma daya daga cikin nau’ukan kayan kamshi da ake amfani da su don kara wa abinci da abin sha kamar su shayi da sauran su karin dandano da kuma kamshi.

Wajen sarrafa itacen na kirfa, akan shanya su bushe ne, kuma da zarar sun bushe sukan kanannade inda ake rika kiran su da sandunan kirfa ko bawon kirfa.

Amma kuma, ana iya nika wadannan sanduna na kirfa zuwa gari mai laushi, wanda kuma yana da wani irin kamshi da dandano na musamman.

Ana kuma samun itacen na kirfa ko cinnamon a ko ina a kasuwannin duniya a manya da kananan shaguna, musamman wurin masu sayar da kayan kamshi da na shayi.

Yanzu haka kamfanonin sarrafa kayan kamshi da ganyen shayi kan sarrafa kirfa ta hanyoyi daban-daban ta yadda mutane za su samu saukin amfani da shi a gidajen su.

Don haka akan sami kirfa a cikin kwalaye masu dauke da jakunkunan tsome irin na ganyen shayi, kana akwai garin shi da akan samu a cikin mazubai don saukin amfani wurin sarrafa nau’ukan abinci.

Mutane da dama kan jefa itacen na kirfa a cikin dahuwar nama ko miya ko kunu, da shayi har ma da irin su dafa-dukan shinkafa da sauran su, a wasu lokutan kuma akan yi amfani da garin kirfa din wajen kwabin cincin da kuma kek don kara dandano da kamshi.

Nau’ukan kirfa ko cinnamon

Kirfa ko kuma cinnamon ya kasu kashi biyu: Akwai Ceylon cinnamon da a kimiyyance ake kira (Cinnamomum verum) da kuma ake yi wa lakabi da “cinnamon na ainihi”, da Cassia ko Chinese cinnamon da shi kuma a kimiyyance ake kira (Cinnamomum aromaticum).

Ana samun Ceylon cinnamon daga kasar Sri Lanka, ta wani gefen kuma Cassia ko kuma Chinese cinnamon ya samo asali daga kudancin kasar China. Nau’in Cassia cinnamon ya fi saukin samu da kuma araha a kan Ceylon cinnamon.

Saboda tsananin tsadar Ceylon cinnamon an fi samun shi a shaguna na musamman, da hakan kuma ya sa akasarin cimaka a Amurka – kamar su burodi da fanke – suka fi kunsar cassia cinnamon na kasar China mafi saukin kudi.

Mutane da dama kan yi amfani da cinnamon a cikin nau’ukan cimaka na zaki. Kamshin da yake da shi na musammanin na faruwa ne saboda yana kunshe da sinadarin cinnamaldehyde.

Amfanin kirfa ko cinnamon ga lafiyar jikin dan adam

Kamar sauran kayan kamshi, masana da dama a fadin duniya sun gudanar da bincike kan kirfa wanda ya nuna cewa baya ga amfani da shi a dakunan dafa abinci na gidajen jama’a, tana kuma da matukar dimbin amfani ga lafiyar jikin dan adam.

Masanan sun bayyana cewa hakan na faruwa ne saboda abubuwan da kirfa take kunshe da su ya sa yake da karfin samar da amfani da dama ga lafiyar jikin dan adam.

Sun kuma gano hanyoyi daban-daban na amfanin da yake da shi ga lafiyar jikin dan adam.

Galibi dai mutane na daukar kirfa ko kuma cinnamon a matsayin kayan kamshi ne kawai ba tare da sanin amfanin da yake da shi baya ga lafiyarsu.

Kamar sauran kayan kamshin dai, mata ne akasari suka fi amfani da kirfa ta hanyoyi daban-daban.

Malama Hauwa’u Rabi’u ta bayyana cewa kirfa na kara wa abinci da kuma shayin da take dafawa dadin dandano da kamshi, ko da yake takan hada itacen da wasu nau’ukan kayan kamshi a ciki.

“Sai dai ko da na hada shi da sauran kayan kamshin, za ka ji kamshim kirfa na fita daban idan kana shan shayin ko kuma ma a lokacin da ake dafa shi,” in ji ta.

Hauwa ta kuma ce ta dade tana amfani da shi amma sai daga baya ta kara fahimtar amfaninsa a jikin dan adam daga irin bayanan da take karantawa da kuma sauraro daga masana.

”Hakan ya sa na kara yawan yadda nake amfani da ita, ba sai a shayi ko wajen dahuwa ba, na kan zuba garin kirfa a cikin madara in sha amma ba a koda yaushe ba,” a cewarta.

Malama Safinatu, mai shekaru 47, ta bayyana cewa tana amfani da garin kirfa wajen gyaran fatar jiki musamman fuska, da kuma itacensa wajen dafa shayi ko kuma ta kan jefa a cikin dahuwa.

”Idan na kwaba garin kirfa da zuma, na kan shafa a fuskata na dan wani lokaci saboda yana taimaka wa wajen gyara fata, kuma na gwada na ga hakan,” in ji ta.

“Saboda kamshinsa kuma na kan kurkure baki da ruwan dumin da na zuba garin kirfa, yana magance warin baki sosai”.

Amma ta ce wajen dafa shayi ba kirfa kadai zalla take amfani da shi ba, ta kan hada da wasu kayan kamshin.

“Saboda idan ka hada da sauran kayan kamshi kamar su kanumfari da citta da habban ko cardamom da sauransu, ya kan bayar da dandano da kamshi daban-daban mai gamsarwa,” in ji Safina.

Sakamakon binciken masanan dai ya rika fadada ta hanyoyin wallafe-wallafen makaloli a mujallun kiwon lafiya daban-daban, da kuma shafukan sada zumunta da miliyoyin jama’a ke amfanin kirfa ko cinnamon.

Irin wadannan mujallu da BBC ta yi nazari a kai game da cinnamon din sun hada da mujallar kiwon lafiya ta Healthy ta Birtaniya, da mujallar Healthline ita ma ta Birtaniya, da kuma mujallar Medical News Today ta Amurka wadanda ke bibiyar binciken masana kan al’amuran da suka shafi lafiyar al’umma a fadin duniya.

Cikin wasu muhimman makaloli da suka shafi amfanin kirfa ko cinnamon har na wacce Miss Yvette Brazier, babbar Editar mujallar Medical News Today, ta wallafa a watan Janairun shekarar 2020 tare da taimakon Miss Katherine Marengo, kwararriya a fannin abinci mai gina jiki daga Jami’ar Jihar Louisiana.

Ga kuma wasu daga cikin amfanin kirfa din:

Karfafa garkuwar jiki: Masana sun ce kirfa na cikin nau’ukan kayan kamshin da ke taimakawa wajen kara bunkasa garkuwar jikin dan adam da ke bayar da kariya daga saurin kamuwa da cututtuka.

Radadi da zafin jiki: Tana kunshe da wasu sinadarai da ke kashe kwayoyin cuta da kan yi tasiri wajen magance radadin da zafin jiki.

Hawan jini: Yana rage matsalar cutar hawan jini.

Ciwon suga: Kirfa ko cinnamon na taimakawa wajen rage sukarin cikin jinin dan adam da ke haddasa cutar suga ko diabetes mataki na biyu.

Yana kuma magance matsalolin gudanawa da sarrafa abinci a cikin dan adam.

Cutar kansa: Bincike da dama sun nuna cewa sinadaran cinnamaldehyde biyu da ke kunshe a cikin kirfa na yin tasiri wajen yakar cutar kansar hanji, da ta jini da sauransu in ji masana.

Sanyin kashi ko gabobi: Sinadari mai karfi na manganese da masana suka gano a cikin kirfa ka iya taimakawa wajen inganta haduwar tsoka a jikin kasussan dan adam, da kan magance matsalar ciwon gabobi da sanyin kashi.

Rage kiba: Masana sun bayyana cewa hada garin cinnamon da zuma kadan a cikin kofin ruwan dumi a sha kafin karin kumallo ko kafin kwanciyar barci da dre ka iya hana kitse taruwa don rage kiba.

Magance cututtukan fata: kamar kurajen fuska, da kyasfi da sauransu – akan kwaba garin kirfa da zuma a shafa.

Magance maikon jini marar kyau (cholesterol): Kirfa ka iya taimakawa wajen rage mummunan tasirin da cin abinci mai maiko ko kitse ke yi wa lafiyar jikin dan adam.

Kada a wuce gona da iri

Duk da dimbin amfanin kirfa da masana da dama da suka bayyana, sun kuma yi gargadin cewa idan aka wuce gona da iri wajen amfani da shi zai iya haifar da wasu illoli saboda irin sinadaran da yake kunshe da su masu karfi.

Hakan ne ya sa suka bayyana cewa mutane su rika yin la’akari da yawan adadi da kuma tsawon lokutan da suka kamata a rika amfani da kirfar ko cinnamon din wato a bisa daidai yadda bukatar hakan ta taso.

Please share after reading

Don’t edit don Allah

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!