YADDA ZAKA SAYI DATA A FARASHI MAI SAUKI A LAYIN MTN
Assalamualaikum barkan mu da sake saduwa daku a wannan lokacin a yau insha Allahu zaku kawo mu yadda zaku sayi data a farashi mai sauki a layin MTN
Duba da wanan lokacin da muke ciki yanda yanzu ana yawan amfani da data kuma datar tayi tsada wasu ma siyan datar ya gagare su wannan dalili ne yasa muka binciko muku wasu hanyoyi guda uku da zaku iya siyan data daidai aljihun ku ma’ana a farashi mai sauki.
Idan kuna son siyan data 1.2GB akan Naira 150 kacal da farko dole sai kun kan tsarin mPlus
idan baka tsarin mPlus kuma kana son komawa tsarin domin samun damar cin wannan garabasar zaka danna *123# bayan ka danna saika zabi inda akasa Tariff plan kana shiga zakaga mPlus sai kayi join.
Bayan kayi join idan kana son siyan wannan datar 1.2GB akan 150 zaka danna 3442#
Karin bayani game da mPlus shine idan ka siya datar 1.2GB ba zatayi amfani ba dole sai kayi amfani Vpn Stark sannan zatayi amfani zaka iya amfani da
Samsung max, HA Tunnels plus, HTT Injector, epory for Android and others.
Idan kana son siyan data 1.5GB akan Naira 200 kacal zaka danna 13188# akan layinka na MTN
Idan kana son siyan data 2GB akan Naira 500 kacal zaka danna 1212# akan layinka na MTN
Wannan sune sabin hanyoyin da muka binciko muku wanda zaku iya samun garabasar data a farashi mai saukin gaske
kudai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa na kimiyya da fasaha
mungode