YADDA ZAKI SAMOSA CIKIN SAUKI

ABUBUWAN BUKATA

  • fulawa
  • alayyahu
  • kwai danye
  • albasa
  • gishiri
  • mai

Zaki samu fulawanki kijuyeta aguri mai tsabta kisaka mata gishiri kadan sai mai kamar cokali 3 kizuba ruwa kikwabata da tauri kimurzata sosai ajiyeta agefe sai kisamu kaskun suyarki kizuba mai kadan badayawa ba zuba yankakkiyar albasarki idan tafara soyuwa sai kijuye yankakken alayyahunki saka dan dano da kayan kamshi kirufe zuwa kamar minti biyar sai kibude kijuya fasa kwanki kisaka masa dakakken masoro kikadasa sosai sai kijuye aciki kirufe kamar zuwa 3 minut sai kibude kijuya kitsaya kina juyawa har yasoyu yamiki yadda kike bukata zakiji wani kalan kamshi natashi juye ki ajiyesa agefe dauko fulawanki kiraba kashi 6 sai kidinga daukan kowane dayan yanka kina yimasa fadi dahaka har kiyiwa kowanne sai kidauko dayan wanda kikayiwa fadi kisaka masa mai kadan sai kuma kibarbada masa fulawa kidora daya akan wanda kika sakawa fulawa haka zakiyiwa kowanne har kihadasu guri daya sai kuma kikara yimusu fadi daga nan sai kigasa zuwa 5 minut kisauke sai yankasa zuwa gida 4 kina baresa kinga kowanne yanka 1 zaibaki 6 kenan sai kina diban hadinnan naki na alayyahu kixubawa sai kinadasa kamar dankwali kisaka fulawanki da kika dama da ruwa da kauri kisakata kimanne bakin dahaka har kigama daga kinkare sai kidora manki akan wuta idan yayi zafi sai kisoya enjoy dadi ba’a magana

Related Articles

Please share after reading

Don’t edit don Allah

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!